Man Utd da Arsenal na gogayya kan Gutierrez, Manyan ƙungiyoyi na rububin Mastantuono

Man Utd da Arsenal na gogayya kan Gutierrez, Manyan ƙungiyoyi na rububin Mastantuono

Manchester United ta kara damara a kan zawarcin matashin dan bayan Girona Miguel Gutierrez kuma tana sa ran yin galaba a kan Arsenal wajen sayen dan bayan dan Sifaniya mai shekara 22 a bazaran nan. (Mirror, daga TeamTalk)

Real Madrid na sa ido a kan dan wasan tsakiya na River Plate Franco Mastantuono, dan Argentina mai shekara 16, wanda Chelsea da Paris St-Germain ma ke sa ido a kanshi. (Fabrizio Romano)

Barcelona da Manchester City ma na sha'awar Mastantuono, wanda kwantiraginsa ya tanadi sayar da shi a kan yuro miliyan 45. (Sport)

Manchester United ta tuntubi Palmeiras a kan matashin dan wasanta na gaba, Thalys, dan Brazil mai shekara 19, wanda har yanzu bai ma fara buga wasansa na farko ba ma a babbar tawagar kungiyar. (TeamTalk)

Watakila Inter Milan ta nemi Anthony Martial idan kwantiraginsa ya kare da Manchester United a bazaran nan - idan har kungiyar ta Italiya ta kasa samun dan gaban Iceland Albert Gudmundsson, daga Genoa. (Gazzetta dello Sport )

Brighton ba za ta nemi ta sake daukan Ansu Fati ba bayan aron da ya tafi can daga Barcelona amma kuma Wolves, da Valencia, da kuma Sevilla kungiyoyi ne da matashin dan Sifaniyan zai iya zuwa a bazaran nan. (Sport )

Everton za ta bukaci sama da fam miliyan 40 domin sayar da Dominic Calvert-Lewin, na Ingila a bazaran nan. (Football Insider)

Luton ta kara nuna sha'awarta a kan mai kai hari na Blackburn Sammie Szmodics na Jamhuriyar Ireland, amma kuma tana fuskantar gogayya daga Brentford. (Sun)

Watakila Amadou Onana ya bar Everton a bazaran nan, inda kungiyar ke sa ran samun daga fam miliyan 50 zuwa 60 a kan dan wasan na tsakiya na Belgium. (Football Insider)

Kungiyoyin Bundesliga na sha'awar sayen dan gaban Tottenham Troy Parrott, na Jamhuriyar Ireland, mai shekara 22, wanda a kakar nan yake zaman aro a Excelsior ta Holland. (Football Insider)

Dan bayan Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, ya ce cin wasanni a Everton, ne a gabansa, kuma yana kawar da duk wata jita-jita a game da makomarsa, inda ake danganta shi da Manchester United. (Liverpool Echo)

Juventus ta cimma yarjejeniya ta baka da Thiago Motta a kan kociyan na Bologna ya zama sabon kociyanta - kuma dan wasan tsakiya na kungiyar ta Bologna Lewis Ferguson, na Scotland kila ya bi shi. (Calciomercato)

Dan wasan gaba na gefe na Italiya Nicolo Zaniolo na son komawa gasar Serie A, idan yarjejeniyar aronsa daga Galatasaray zuwa Aston Villa ta kare a bazaran nan, kuma tuni Fiorentina da Napoli suka yi magana a kanshi. (Gazzetta dello Sport )

Post a Comment

Previous Post Next Post