Kissar Dhul-Qarnaini da yajuju da majuju Kashi Na Uku (3)
Sunan Littafin: The Story Of Alkur'an
Marubuci: Ibn Kathir
Fassara Saliadeen Sicey
Abu Ishaq As-Subai’i ya ruwaito daga Amru Ibn Abdullah Al-Wada’i: “Na ji Mu’awiya yana cewa: Mutane hudu ne suka yi mulkin kasa: Sulaiman Ibn Dawud Annabi (AS), ZulQarnain, sai wani mutum daga cikin mutanen Hulwan, ya ce: Al-Khadir sai ya ce: A’a.
Az-Zubair Ibn Bakkar ya ruwaito cewa Sufyan Ath Thawri ya ce: “Na tabbata mutane hudu ne suke mulkin duniya baki daya: biyu daga cikinsu sun kasance muminai, sauran biyun kuwa kaf*irai ne. Muminai biyu su ne: Annabi Sulaiman da Zul-Qarnaini. Kuma, kafi*ran biyu su ne: Namrud da Bikhtinassar.” Haka Sa’id ya ruwaito.
Ishaq Ibn Bishr ya ruwaito daga Sa’id Ibn Abu Urubah daga Qatadah shi kuma daga Al-Hasan yana cewa: “Dhul-Qarnain sarki ne bayan Namrud, shi musulmi ne salihai mai takawa mai mulkin gabas da yamma, Allah Ta’ala ya tsawaita ransa kuma ya ba shi nasara a kan makiya da kuma yin riko da dukiyoyinsu, ya rinjayi mutane, ya yi tafiya a cikin kasa har ya isa karshen gabas da yamma. Ka ce : "Zan karanta muku wani abu daga lãbãrin ZulQarnain, Muqatil ya yi da’awar cewa ya kasance yana cin kasashe yana tara dukiya, kuma ya kasance yana baiwa mutane zabi biyu: ko su rungumi addinin tauhidi su bi shi, ko a kashe su.
Ibn Abbas, da Mujahid, da Sa’id Ibn Jubair, da ‘Ikrimah, da Ubaid Ibn Ya’ la, da As-Sadyi, da Qatadah da Ad-Dahhak suka ce: {kuma Muka ba shi sigar komai}, watau ilimi. Qatadah da Matar Al-Warraq sun ce: Wannan yana nufin alamomin ƙasa, wurare, matakai. Abdur Rahman Ibn Laid Ibn Aslam ya ce: wannan yana nufin harsuna kamar yadda ya kasance ba ya yakar mutane saiya ya fara magana da su da harshensu. Mafi yuwuwa kuma tabbataccen bayani shine ya san duk hanyar da zai iya cimma nasarar sa, Kamar yadda ya saba Mulkar kowane yanki da aka ci da yaki, abubuwan da suke ba shi damar kwace yankin na gaba, da sauransu.
Wasu malamai daga Ahlul Kitabi (Kiristoci da Yahudawa) sun ambaci cewa ya shafe shekaru dubu daya da dari shida yana yawo a cikin kasa yana kiran mutane zuwa ga bautar Allah Madaukakin Sarki wanda ba shi da abokin tarayya a cikin Mulkinsa. Amma, da alama akwai wuce gona da iri wajen ayyana tsawon wannan lokacin, kuma Allah ne Mafi sani!
Fadin Allah {Sai ya bi hanya har a lokacin da ya isa mafadar rana} wato ya isa wurin da babu wanda zai iya tsallakewa, sai ya tsaya a gefen teku daga yamma a wani waje da ake kira Oqyanu a cikin tsibiran da ake kira Al-Khalidat "Masu Dawwama". A can, ya iya kallon faɗuwar rana. {Ya same ta tana faduwa a cikin wani marmaro na ruwan bakin tabo (mai zafi)}, watau teku ko kamar yadda wanda ya tsaya a bakin teku zai ga kamar rana ta fadi a cikin teku. Don haka ya ce {ya same ta}, kamar yadda yake tunani.
Imam Ahmed ya ruwaito bayan Yazid Ibn Hamn bayan Al-Awwam Ibn Haushab yana cewa: “Wani bawan Abdullahi Ibn Amr bayan Abdullahi ya ba ni labari cewa: “ Manzon Allah (SAW) ya dubi rana, sai ya zauna ya ce: "ba domin hana ta da umurnin Allah ba, da rana kone abin da ke cikin kasa gaba daya.
An ruwaito bayan Ubaid Ibn Umair da dansa Abdullahi da wasunsu cewa Zul-Qarnain ya yi aikin hajji da kafa. Da jin labarin haka sai Ibrahim (AS) ya gamu da shi, kuma a haduwarsu ya roki Allah saboda shi, ya yi masa nasiha. An ce kuma an kawo masa doki ya hau, sai ya ce: “Ba na hawa (a bayan dawaki) a kasar da Annabi Ibrahim (AS) yake cikinta. Don haka sai Allah Ta’ala ya hore masa gizagizai, kuma Ibrahim (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya yi masa bushara a kan haka. Gizagizai sun kasance suna kai shi duk inda ya ga dama. Allah Ta'ala yana cewa: {Sai kuma ya bi (wata hanya). Har a lõkacin da ya isa a tsakãnin duwãtsu biyu, ya sãmi waɗansu mutãne a gabãninsu (duwãtsu biyu) An ce su Turkawa ne, ’yan uwan Yajuju da Majuju. Duk da haka, suka gaya masa cewa Yajuju da Majuju suna zaluntar su kuma suna yi musu barna a ƙasarsu. Suka ba shi lada saboda ya gina katanga ya hana su kai farmaki a kansu. Sai ya ki karbar ladan da suka ba shi, yana mai cewa ya wadatuwa a cikin abin da Allah Ta’ala Ya ba shi, don haka {Ya ce: ((Dukiya da mulki) da Ubangijina Ya tabbatar da ni a cikinsu su ne mafi alheri (fiye da ladan ku)}.
Sai ya umarce su da su zo da shi mutane da kayan aikin da za su Gina katanga a tsakaninsu daga wannan wuri da ke tsakanin duwatsun dutse guda biyu. Ya gina ta da ƙarfe da narkakkiyar tagulla: ya sanya baƙin ƙarfe maimakon tubali da narkakkiyar tagulla a maimakon yumbu, Allah Ta'ala Ya ce: {Saboda haka (Yajuju da Majuju) ba su iya rusheta ba} {ko su sara ta da gatari sai lokacin da Ubangijina ya so} watau a lokacin da Ya yi niyyar ruguza ta (Yajuju da Majuju) su fita suyi yaki da mutane a kusa da lokacin tashin kiyama {za ta rushe} wannan babu makawa zai auku. . Kamar yadda yake cewa {Kuma wa'adin Ubangijina ya kasance gaskiya ne}, kuma {Har zuwa lokacin da aka saki Yajuju da Majuju (daga katangesu), kuma su ke gangarowa daga kowane tudu. Kuma wa'adi na gaskiya (Rãnar ¡iyãma) ya kusata. Sa'an nan kuma (idan aka tãyar da mutãne daga kaburburansu) kanã ganin idãnun kãfi**rai sunã kallo a cikin firgici. (Suka ce): “Kaitonmu! Kuma lalle ne, haƙĩƙa, mun kasance, gafalallu, kuma mun kasance azzãlumai} . (Al-Anbiya’i, 96, 97) Allah Ta’ala yana cewa: { Za mu bar su su yi ta girgiza junansu watau ranar da Yajuju da Majuju za su fito, { kuma a yi busa a cikin kaho, sai mu tara su (halitta gaba daya}.
Zan ci gaba ✍️
A lura babu dadi ku kari danayi a cikin wannan Rubutu. Daga kashi na daya har zuwa wannan na uku daga littattafan Ibn Kathir Na The Story Of Alkur'an na Fassara.
Post a Comment