Kissar Dhu al-Qarnayn da Yajuju da Majuju Kashi Na Biyu (2) (Suratul Kahfi)
Menene sunansa?
Malamai sun yi sabani game da sunansa. Az Zubair Ibn Bakkar ya ruwaito bayan Abdullahi Ibn Abbas (Allah Ya yarda da shi): cewa: Sunansa Abdullahi Ibn Ad-Dahhak Ibn Ma’d; ko Mus'ab Ibn Abdullah Ibn Qinan Ibn Mansur Ibn Abdullah Ibn Al-Azd Ibn Ghauth Ibn Nabt Ibn Malik Ibn Zaid Ibn Kahlan Ibn Saba' Ibn Qahtan.
Ya zo a cikin wani Hadisi cewa shi dan kabilar Himyar ne, kuma mahaifiyarsa yar Rum ce, kuma ana kiransa da masanin Falsafa don daukakar tunaninsa. Sai dai As-Suhaili ya ce: Sunansa Marzaban Ibn Marzabah. Ibn Hisham ya fada wanda ya ambata a wani wurin cewa sunansa: As-Sa’b Ibn Dhi Mara’id kakan Tababi’ah ne kuma shi ne ya bayar da fatawar ga Ibrahim (AS) ya tabbata a gare shi) dangane da gina rijiyar As-Sab.
Aka ce: Shi ne Afridun Ibn Asfiyan wanda ya kashe Ad-Dahhak. Al-Qass Ibn Sa'idah Al-Iyadi yana cewa a cikin shahararriyar hudubarsa: Yaku mutane Ayad Ibn As-Sa'b! Dhul-Qarnain ya yi mulkin yamma da gabas, ya mallake Aljanu da mutane, kuma ya rayu tsawon shekaru dubu biyu. Duk da haka, duk wannan ya kasance kamar ƙyaftawar ido.
Ad- Daraqutni da Ibn Makula sun ambata cewa sunansa Hirmis, ko Hirwis Ibn Qitun Ibn Rumi Ibn Lanti Ibn Kashaukhin Ibn Yunan Ibn Yafith Ibn Nuh (Alaihis Salam) amma Allah ne mafi sani!
Ishaq Ibn Bishr ya ruwaito bayan Sa’id Ibn Bashir daga Qatadah yana cewa: “Alexander (ana kiransa) Zul-Qarnaini, mahaifinsa shi ne Kaisar na farko, kuma yana daga cikin zuriyar Sam Ibn Nuhu (AS).
A wannan hasashe ya kamata a banbance tsakanin mutane biyu da ake ce wa Zul-Qarnaini. Na farko shi ne Zul-Qarnaini mai tsoron Allah yayin da na biyu Alexander Philips Ibn Masrim Ibn Hirmis Ibn Maitun Ibn Rumi Ibn Lanti Ibn Yunan Ibn Yafith Ibn Yunah Ibn Sharkhun Ibn Rumah Ibn Sharfat Ibn Tufil Ibn Rumi Ibn AI-Asfar Ibn Yaqz Ibn Al. -'lis Ibn Ishaq Ibn Ibrahim (AS). Bugu da kari Al-Hafiz Ibn Asakir ya bayyana wannan tsatson a cikin Tarikh dinsa (Tarihi). Yace shi ne shugaban Masadoniya, da Girka, da Masar wanda ya kafa Iskandariya. Ya zo bayan Zul-Qarnaini na farko da wani lokaci mai tsawo. Shekara dari uku kenan kafin Annabi Isa (AS). Wazirinsa shi ne sanannen mai ilmin Falsafa Artatalis. Haka kuma, shi ne ya kashe Dara Ibn Dara, ya mallake sarakunan Farisa, ya kwace musu kasashensu. Sai dai mun ja hankalin mai karatu a kan haka, domin da yawan mutane suna ganin cewa mutanen biyu da ake ce wa “Dhul-Qarnain” ni ne, wanda wannan kuskure ne babba domin akwai babban bambanci tsakanin su biyun. Na farko shi ne mai tsoron Allah ne, salihi mai bautar Allah Madaukakin Sarki, kuma shi sarki adali ne wanda wazirinsa shi ne mutumin kirki, Al-Khadlr. Haka kuma wasu malamai sun ce shi ma Annabi ne. Alhali, na karshen mushriki ne wanda wazirinsa ya kasance masanin falsafa kamar yadda aka ambata a baya. Bugu da kari, lokacin da ya shiga tsakaninsu su biyu ya wuce shekaru dubu biyu. Don haka babu wanda zai kasa sanin bambance-bambancen da ke tsakanin su face jahili wanda bai san komai ba!
Fadin Allah: {Kuma suna tambayarka game da Zul-Qarnaini} ayar ta sauka ne lokacin Quraishawa suka nemi Yahudawa su gaya musu wani abu da za su tambayi Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) don su gwada shi. Yahudu suka ce musu: Ku tambaye shi game da wani mutum wanda ya yi tafiya a cikin ƙasa, da kuma game da wasu samari waɗanda suka yi tafiya, ba wanda ya san abin da ya same su? Daga nan sai Allah Ta’ala ya saukar da labarin Ma’abota kogo (Asahabul Khafi) da na Zul-Qarnaini. Don haka sai ya ce: {Ka ce: Zan karanta muku wani abu daga labarinsa}, watau isasshen labari game da shi da matsayinsa. Sannan ya ce: {Lallai ne Muka tabbatar da shi a cikin kasa, kuma Muka ba shi arzikin komai}, wato Allah Madaukakin Sarki Ya fadada mulkinsa, ya azurta shi da abin da zai iya ba shi damar samun abin da yake so. Qutaibah ya ruwaito cewa, an taba tambayar Ali Ibn Abu Talib (AS) game da Zul-Qarnaini: ta yaya ya kai gabas da yamma? Sai Ali ya ce: An hore masa Gizagizai, aka azurta shi da abin da ake bukata (na kowane abu), kuma aka tsawaita masa game da haske. Ali ya kara da cewa: Kuna so in ci gaba? Sai mutumin ya yi shiru, sai Ali (Allah Ya yarda da shi) ya yi shiru.
A Lura Ba Ra'ayi na, ko ragi ko kari akan wannan kissa da nake rubutawa, face abinda na gani a rubuce. Allah Masani. Zanci Gaba InshaAllah .
Post a Comment