Mai dokar Kasa tace akan wadanda suke cutar Mutane da Sunan Investment wanda daga karshe zakaga sun gudu da kudin mutane





• Mai dokar Kasa tace akan wadanda suke cutar Mutane da Sunan Investment wanda daga karshe zakaga sun gudu da kudin mutane
_____________________________________________________
Tabbas an dade ana cutar mutane da Sunan Investment, ace ka zuba kudi Misali Dubu 30, in the Next 2 weeks zaka samu Dubu Dari 2, or something like that, so irin wannan Financial Business din dokokin Nigeria sun haramta shi kuma sun tanadi ukuba ga duk wanda aka kama ya aikata wannan laifin, dan haka ba ma wai wanda ya Samar da Financial business din ba, kai ma da kaje kayi Investment din sai an hukunta ka, babu ruwan kotu da cewa wai ai bakasan yin hakan laifi bane ba, domin kuwa Kotu tana cewa “Ignorantia Juris non excusat” wato rashin sanin doka ba hujja bane, Saboda irin wannan Financial Business din yana haifar da ci baya mai yawa da asara ga tattalin arzikin kasa, domin kuwa NDIC sun kiyasta cewa anyi asarar kimanin Naira Biliyan 18 (N18 billion) lokacin da aka rufe MMM a shekarar 2016. To mu duba dokokin kasar mugani me suke cewa.

Sashi Na 67(1) Na Investment and Securities Act, 2007 da Sashi Na 1(5)(a) dana 58 Na Banks and other Financial Institutions Act, 2004, sune suka haramta irin wannan Financial Business din.
Haka ma idan muka duba Shari'ar da akayi tsakanin Mekwunye da Lotus Capital Ltd. & ORS zamuga kotu ta haramta irin wannan Financial Business din.
Dan haka ba'a yarda mutum yayi wannan hada-hadar ba har sai ya nemi izini daga babban bankin Nigeria (CBN) kamar yadda yazo a Sashi Na 59 Na Banks and other financial Institution act, 2004. To su kuma masu yin irin wannan Financial Business din suna yin abinsu ne gaba gadi ba tare da sun nema izini daga babban Bankin kasa ba, saboda daman sun San cutar mutane za suyi, don haka babu bukatar Babban Bankin kasa yasan da zaman su.

Menene Hukuncin wanda ya aikata laifin ?

Sashi Na 67(2) Na Investment and Securities Act, 2007 yace: Duk wanda aka kama ya aikata wannan laifin idan Kampani ya yaudara ya gudu masu da kudi, to zai biya tarar kudi Naira dubu Dari 5, idan kuma ba Kampani ya yaudara ba daidaikun mutane ne (Individuals) to zai biya tarar kudi Naira dubu Dari.

Saidai Shikuma Banks and other Financial Institutions Act, 2004, hukuncin sa ya bambanta dana Investment and Securities act, 2007, don kuwa shi yazo da hukuncin dauri ne Na gidan Kaso har na tsawon Shekara 5 da kuma tarar kudi Naira Miliyan Daya (N1 Million) ga duk wanda aka kama da wannan laifin.
Duba Sashi Na 59(6)(a)(b) Na Banks and other financial Institutions act, 2004, domin tabbatarwa.

To saidai tambayar Shine: Ko kudin mutum zasu iya dawowa ?

A gaskiya kotu ba zata bibiyar maka kudin ka ba, domin kuwa transaction din aslan ya saba ma doka, Supreme Court kuma tayi hukunci da cewa: duk wani Contract da mutum ya kulla ta haramtacciyar hanya to koda an cuceshi ko an yaudareshi bayada hurumin da zaije kotu Neman hakkin shi, saboda tun wajen kulla Contract din an kulla ta ne ta haramtacciyar hanya, a yaren kotu wannan shi ake kira da: “Ex turpi causa non oritur actio” Duba Shari'ar da akayi tsakanin Onyiuke III da Okeke, Per Alexander, C.J.N. (P. 9, paras. B-D) da kuma Shari'ar da akayi a Court of Appeal (Kotun daukaka kara) tsakanin Albia Trading GMBH & ANOR da Madunka Int’l Ltd & ANOR, Per Mbaba J.C.A (Pp. 25-27, paras. F-C)


Post a Comment

Previous Post Next Post