Babu Mahalukin Da Zai Iya Ganin Jinjirin Watan Shawwala A Gobe, Cewar Masana
Daga Shuaibu Abdullahi
Masana ilimin wata sun tabbatar da cewar cikin iKon Allah babu wani mahaluki da zai iya ganin watan Shawwal a gobe litinin, wannan ne ke tabbatar da cewar Azumin wannan shekarar 30 za a cika cif-cif.
Sun tattara alkaluman ne bisa dogaro da sashin ilimin bindiddigi da baje fikirar ilimi da suka saba yi a kowane wata ba na Ramadan ba kawai, kuma watan Shawwal zai bayyana ranar Talata.
Sanarwar ta ce za a haifi watan Shawwal ne gobe Litinin bayan rana ta fadi da misalin karfe 7:21 hakan ke nuna cewar ba zai bayana sai ranar Talata, kuma lokacin da zai bayyana an haife shi da awanni 23 da 'yan sakwanni.
Me za ku ce?
Post a Comment