Tabbas bana azumi Talatin (30) za ayi, domin baza aga watan Shauwal شوال ba a yau Litinin 29 ga Ramadan رمضان a Nijeriya da Saudiya, bana haƙiƙa sai an cika {30}



Tabbas bana azumi Talatin (30) za ayi, domin baza aga watan Shauwal شوال ba a yau Litinin 29 ga Ramadan رمضان a Nijeriya da Saudiya, bana haƙiƙa sai an cika   {30}

بسم الله الرحمن الرحيم، 
اللهم صل على سيدنا محمد وعلى آله وصحبه وسلم،
    
                             29/09/1445,
                            08/04/2024,

ƘARSHEN WATAN RAMADAN. رمضان

DA FARKON WATAN SHAUWAL. شوال

NA SHEKARAR 1445 HIJJIRIYYA, WACCE TA YI. DAI-DAI DA (2024) MILADIYYA, 
 
Lissafin wata akan ilimin (HISABI) wato (FALAKI) da ƙa'ida ta shari'a.
 
                              Daga, 
          Gwani Mai Ismi Foundation 
       
             +234 ~0813 333 2289
 
Daga farkon watan Almuharram zuwa yau Litinin Takwas  ga watan huɗu shekara ta, dubu biyu da ashirin da huɗu 08/04/2024, Miladiyya.
kwanakin shekarar Hijjiriyya an sami kwana ɗari biyu da Sittin da biyar (265)

Wato daga ɗaya gawatan Almuharram zuwa  Ashirin da tara. 29 ga watan RAMADAN.

Sannan daga farkon watan Almuharram na Shekarar farko ta hijjara zuwa talatin, ga watan RAMADAN na shekara ta dubu ɗaya da ɗari huɗu da arba'in da biyar (30/09/1445)
watannin da suka cika suka yi. kwanaki talatin-talatin (30) su dubu tara ne, da ɗari ɗaya da casa'in da Takwas (9,198)
Watannin kuma da suka yi, nuƙusani kwana Ashirin da tara-tara (29) su dubu takwas ne, da ɗari ɗaya da Talatin da Tara. (8,139) idan kuma an haɗa yawan adadin waɗanda suka yi, 30 da waɗanda suka yi, 29
9,198+8,139= zaibaka 17,337 

In karaba da goma shabiyu. 17,337÷12 zai baka shekaru 1444, da wata 9, dai-dai. 

Shekarar musulunci, tana ɗauke da kwana ɗari uku da hamsin da huɗu da awa takwas da minti arba'in da takwas. 354/8/48
 
KAMAWAR WATAN SHAUWAL (شوال) ZA'A SAMI HAIHUWAR SABON JINJIRIN WATAN SHAUWAL NE. A YAU LITININ 08/04/2024, DA MISALIN ƘARFE 7:22 (PM) NA DARE  A AGOGON NIJERIYA, A ƘASAR SAUDIYA KUMA DA MISALIN ƘARFE 9:22 (PM) NA DARE, ALOKACIN WATA YA YI, MUƘARANA DA RANA WATO ATURANCE (Conjunction) KENAN ACIKIN BURUJIN JAUZA'A (حمل) AKAN DIGIRI, WATO DARAJA GOMA SHATARA  (19°) SANNAN SUN HAƊU AKAN MUNZILAR. BUƊAINI (بُطَيْنِ)

DA LILAI AƘALLAH UKU (3)  DA ZASU SA BAZA A IYA GANIN WATA BA, A YAU LITININ 08/04/2024 
WACCE TA YI DAI-DAI DA, 29/09/1445, 

NA. 1 A YAU LITININ WATAN RAMADAN رمضان ZAI FAƊI DA MISALIN ƘARFE 6:34  (PM)  NA YAMMA ANAN JAHAR KADUNA/NIGERIA, ITA KUMA RANA ZATA FAƊI DA ƘARFE  6:40 (PM) NA YAMMA, BAYAN FAƊUWAR WATAN RAMADAN رمضان A YAU DA MINTI 6 RANA ZATA FAƊI, 

A BIRNIN MAKKA NA ƘASAR SAUDIYA KUMA WATAN RAMADAN رمضان ZAI FAƊI A YAU LITININ DA MISALIN ƘARFE 6:26 (PM) NA YAMMA, ITA KUMA RANA ZATA FAƊI DA 6:38 (PM)  NA YAMMA, BAYAN FAƊUWAR WATAN RAMADAN رمضان DA MINTI 12 RANA ZATA FAƊI A BIRNIN MAKKAH,

NA 2. ALOKACIN DA ZA' NEMI WATAN SHAUWAL A NIJERIYA BA'A MA HAIFI WATAN BA WATO BABU WATAN SHAUWAL A SAMA,  HAKA MA ƘASAR SAUDIYA, LOKACIN DA ZASU FITA DUBAN WATAN SHAUWAL BABU WATAN ASAMA, 

NA 3. DOMIN A NIJERIYA KAMAR YADDA MUKA YI, BAYANI A BAYA DA ƘARFE 7:22 (PM) NA DARE ZA'A SAMI HAIHUWAR SABON JINJIRIN WATAN SHAUWAL, A ƘASAR SAUDIYA KUMA DA MISALIN ƘARFE 9:22 (PM) NA DARE DA GA WANNAN LOKACIN IN DAI ANA SO A IYA GANIN WATA AƘALLAH SAI WATA YA SAMI AWA 18 KAFIN A IYA GANIN SHI DA ƘWAYAR IDO, DA NA URAR BATURE KUMA TA HANGEN NESA 🔭 AƘALLAH YA SAMI AWA 12
     
SABODA HAKA BABU YADDA ZA'AYI A IYA GANIN WATA A NIJERIYA, DA SAUDIYA, A YAU RANAR LITININ  29 GA WATAN RAMADAN, رمضان DOLE IN DAI A SHARI'ANCE NE, BANA AZUMI (30) ZA AYI, DOMIN BAZA AGA WATA BA A YAU, 

SABODA HAKA IDAN ALLAH YA KAIMU, GOBE TALATA 09/04/2024, MILADIYYA. ITA CE ZATA YI, DAI-DAI DA 30/09/1445, HIJJIRIYYA.
        SAI RANAR LARABA 10/04/2024, ITA CE ZATA YI, DAI-DAI DA 1/10/1445, HIJJIRIYYA.

INA FATAN ALLAH YA KAIMU WATAN SALLAH  DA RAI DA LAFIYA YA KUMA KARƁI IBADUN DA MUKAYI ACIKIN WATAN RAMADAN KUMA ALLAH YA ƘARA MANA LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA DA ABINDA LAFIYAR ZATA AMFANA DASHI AMEEN.
                Gwani Mai Ismi Foundation

Post a Comment

Previous Post Next Post