Qissar Dhu al-Qarnayn (A.S) Kashi Na Daya (1).
A Harshen Larabci na Kur'ani "Dhul-Qarnayn" yana nufin "mai ƙaho biyu". Wasu suna fassara wannan da cewa Alexander the Great ne, wanda aka kwatanta shi a matsayin wanda yayi nasarar mallake ƙahoni biyu na duniya, ƙasashen da rana ta ke faɗuwa da kuma wuraren fitowar rana.
Dhu al-Qarnayn, (Da Larabci:ذُو ٱلْقَرْنَيْن, : Ḏū l-Qarnayn ,IPA: [ðuː‿l.qarˈnajn] ;lit."Mai Kaho Biyu") ya zo a cikin Alqur'ani, Surah al-Kahf Ayahta 83–101 a matsayin wanda ya yi tafiya zuwa gabas da yamma kuma ya sanya shamaki tsakanin wasu mutane da Yajuju da Majuju (Da Larabci:يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ, Yaʾjūj wa-Maʾjūj ). A wani wurin kuma, Alkur’ani ya yi bayanin yadda karshen duniya za a sakin Yajuju da Majuju daga bayan shamaki (Katanga) Wasu rubuce-rubucen sun yi hasashen cewa lokacin zai zo kusa qiyama (Yawm al-Qiyāmah).
Ayoyin sun nuna Dhu al-Qarnain ya fara tafiya zuwa iyakar yammacin duniya inda ya ga in da rana ta fadi a cikin wani ruwa mai tabo, sannan ya nufi gabas mai nisa inda ya ga fitowar rana daga teku, daga karshe kuma ya nufi arewa zuwa wani wuri mai cike da ruwa a cikin duwãtsu inda ya sãmi wasu mutãne waɗanda Yãjũja da Majuju suka zãlunta.
Zulkarnaini ya kasance Sarki ne adali a bayan kasa, kuma Salihin bawan Allah ne Musulmi, Ya yi mulkin duk duniya kuma yakarade duniya gabas da yamma yana yada Tauhid da Musulunci, yayi raga-raga da ka**firci da zalunci a bayan kasa. Kuma sarki zulkarnaini yayi zamani ne tare da Annabi Ibrahim Alaihis Salam. A cikin zance mafi inganci.
Malaman tarihi sun ruwaito ra’ayoyi mabambanta akan Zulkarnaini, An ce sarki ne na Daular farisa, an ce Annabi ne, wasu ma sun ce mala’ika ne shi zulkarnainin. An ce yayi rayuwa ne a kasar Himyar zamanin Annabi Musa ko Zamanin Annabi Ibrahim. Sannan an ce katangar da ya gina tana kasar Sin ne wasu suka ce tana cikin Tekun Atalantic wasu kuma sun ce ba’a san inda take ba. An samu sabani mai yawa a cikin tarihin wannan bawan Allah.
Allah Ta’ala ya ambaci Kissar zilkarnaini a al-Kur’ani Mai Girma cikin suratul Kahfi (sura ta 18 aya ta 83 – 98) Allah ya yabe shi da adalci, da girman mulkin da ya hade gabas da yamma. Kuma shi ne ya gina katangar da ta tsare Yajuju-da-Majuju daga barna a cikin duniya.
Kissar Zulkarnaini tana daga cikin tambayoyi Uku da Yahudawa suka sa Mushi**rikan Larabawa suyiwa Ammabi Muhammad (SAWW) tambaya a kai. Lalle kissa ce da ke cike da labarai mabambanta. Kissar na cikin littafan Yahudu da Nasara. Sai dai a matsayin mu na musulumai, za mu iya karanta duk labaran kuma mu saitasu da abinda al-Kur’ani ya kissanta mana.
Shin Annabi ne?
Allah Ta’ala ya yabi Zul-Qarnaini a cikin Alqur’ani mai girma bisa adalcinsa. Ya yi mulkin gabas da yamma da yankuna da yawa inda ya yi wa al'ummarsu mulki da adalci. Mafi kusantar ra'ayi shine cewa shi sarki ne kawai ba Annabi ba.
Game da cewa Mala’ika ne
An ruwaito Shugaban Muminai Umar Ibn Al-Khattab (Allah Ya yarda da shi) ya ji wani mutum yana kiran wani yana cewa: Zul-Qarnaini! Sai (Umar) ya ce: Yi shiru! Shin bai ishe ku ba, ku rada wa kanku sunayen Annabawa, sai ku riki sunayen Mala'iku?
Cewa shi Annabi ne
An karbo daga Abdullahi Ibn Amr ya ce: “ Dhul-Qarnain Annabi ne.
A wata ruwayar kuma Ibn Abbas (Allah Ya yarda da shi) ya fitar da wani rahoto da ya zo da cewa Zul-Qarnaini sarki ne nagari wanda aka sanya aikinsa a cikin littafin Allah (Alkur’ani mai girma); kuma bature ne; kuma Al-Khadir ya kasance wazirinsa, shugaban rundunarsa, kuma mashawarcinsa.
Al-Azraqi da waninsa sun ambaci cewa Zul-Qarnain ya
musulunta a hannun Annabi Ibrahim (AS) kuma ya yi dawafi a dakin Ka’aba tare da shi da dansa Isma’il (AS). . Har ila yau, an ruwaito Ubaid Ibn Umar da dansa Abdullahi da waninsa cewa: Zul-Qarnain ya taka da kafa domin yin aikin Hajji. Da jin haka sai Ibrahim (AS) ya yi masa maraba, ya roki Allah saboda shi, ya kuma yi masa nasiha. Haka nan kuma Allah Ta’ala ya hore wa Zul-Qarnaini gizagizai domin ya kai shi duk inda ya ga dama. Allah ne mafi sani!
Me ya sa aka ce masa "Dhul-Qarnaini" (wato Mai kaho biyu) ?
Wannan lamari ne mai cike da cece-kuce, cewa babu wani tabbataccen dalili da aka sani a baya. Wasu suka ce: yana da wani abu a kansa mai kama da ƙaho biyu. Wahb Ibn Munabih ya ce: Yana da kahon tagulla guda biyu a kansa. (Wannan fassarar tana da rauni sosai)
Wasu malamai daga Ahlul Kitabi (Kiristoci da Yahudawa) suka ce: saboda ya yi mulki a yankunan Farisa da Rum. Kuma aka ce: ya riski hasken farkon fitowar rana a gabas da faduwar ta a yamma kuma ya yi hukunci a kan dukkan abin da ke tsakaninsa. (Mai yiwuwa ra'ayi na karshe gaskiya ne, wato fadin Az-Zuhari).
Ishaq Ibn Bishr ya ruwaito cewa, kakan Umar Ibn Shu’aib ya ce: “DhulQarnain, ya taba gayyatar wani sarki azzalumi zuwa ga tafarkin Allah. Sarki ya buge shi a kai ya karya kahonsa daya. Dhul-Qarnain ya sake gayyatarsa, sai azzalumi ya fasa kaho na biyu. Don haka ake kiransa "Dhul-Qarnain.
Ath-Thawri ya ruwaito cewa, an taba tambayar Ali Ibn Abu Talib (Allah Ya yarda da shi) game da Zul-Qarnain. Sai ya karba masa da cewa: Shi mutum ne shiryaye mai taqawa. Ya kira mutanensa zuwa ga Allah, sai suka buge masa kaho a (gefen kai) sai suka kashe shi. Allah Ta’ala ya tayar da shi, ya sake kiransu, suka sake buge shi a kahonsa na biyu aka kashe shi (a karo na biyu). Allah Ta’ala ya rayar da shi don haka ake kiransa da “Dhul-Qarnaini”. A cikin wasu ruwayoyin kuma, Abu At-Tufail ya ruwaito bayan Ali Ibn Abu Talib ya ce: Shi ba Annabi ba ne, kuma ba Manzo ba ne, kuma ba Mala’ika ba ne, sai dai ya kasance mai tsoron Allah.
Duk ba Ra'ayina ciki face abinda na karanta, Allah shi ne mafi sani. Zan cigaba insha Allah ✍️
Post a Comment