YADDA ZAKA KOYI PROGRAMMING ACIKIN WATA DAYA (1 MONTH) GA MASU BUKATA (BEGINNERS)
Da farko dai, yana da kyau mu fahimta a wannan rubutun zanyi bayani ne akan abubuwan da mutum beginner yake bukata a a matsayin koyon basics na programming wanda zai kaishi ga amsa sunan programmer. To sai dai akwai banbanci sakanin “Developer” da kuma Programmer, shiyasa anan nayi zancen Programmer ba Developer ba. Zama Developer yana matukar bukatar karin abubuwa akan wadannan bayanin da zanyi amma dai sai mutum yazama programmer kan yake zama Developer, dan haka a biyoni a sannu dan karanta bayanin.
SATIN FARKO (RANAKUN FARKO DANA BIYU): A kwana biyu na farko abinda mutun yakamata yayi shine zabar yaren da yakeso ya koya. Zabar yaren da kakeso kakoya abu ne mai matukar mahimmanci, diyawa sababbi a wannan harkar suna samun matsaloli wajen sanin wane yakamata mutum yafara dashi ko ya koya. Mafi yawan lokuta abinda nake fara tambayar mutum shin “Me kakeson yi da in ka koyi Programming din?”, dalilina shine zaka samu wani yanaso ne ya hada Website wani Mobile App, wani Desktop, wani Games da sauransu. Kowanne acikin abubuwan da na irgo akwai yarukansa na musamman, misali idan mutum daga Math ko Statistics yake ma cemar nake ya koyi R da Python domin sune sukafi da cewa dashi, to kaima a matsayinka na beginner kasan asalin abinda kakeso ka koya, idan Web Development ne, ka koyi PHP, idan Mobile App ne ka koyi Java ko Kotlin, idan Desktop App shima kakoyi C# ko Java, idan kuma Game ne Kakoyi C# idan game din babba ne wato Video game zance kakoyi C++ to haka yakamata mutum yayi. Bayan kazabi Language din misali mudauka Web kakeson yi sai kazabi PHP sannan ka karanta bayanai game da PHP ciki harda tarihinsa da yadda aka samar dashi, hikimar hakan shine yayin karantawa zaka hadu da sabbin “Kalmomi” wanda aɗa bakasan dasu ba hakan zai baka damar son sanin menene ma'anarsu. Daga nan, sai kanemo Text Editor da Compilernsa ko kuma dai abinda zakayi amfani dashi wajen running din Program din, tunda dai da PHP muke buga misali zance mutum yayi installing text editor irinsu Sublime Text da sauransu sai kuma Xampp. In kuma language irinsu Java ne sai ayi installing JDK da sauransu sannan sai a koyi yadda za'ayi Configuration na language saboda a tabbatar komai ya saitu in akazo running program din yayi ba tare matsala ba.
SATIN FARKO (RANA NA UKU HAR ZUWA BAKWAI): A rana na uku har zuwa ranar bakwai na sati sai mutum yafara koyon wadannan abubuwan
– Yadda ake printing abu a wannan yaren (misali printing Hello World) da kuma yadda ake shigar da abu wato (Input) (Kwana daya)
– Variable da yadda ake aiki dashi ciki harda baya nan Data types da sauransu (Kwana biyu)
– Operators (Arithmetic, Logical, Comparison da Kuma Unary) (Kwana biyu)
Daga nan satin farko ya kare, sai dai a lokacin da kake koyon yana da kyau kana goda misali daban daban, misali in ka koyi yadda ake printing abu da kuma input, sai kayi ta rubuta program da zai baka damar ko saka 36 state din Nigeria sannan kayi printing, ko program da zai karbi sunan mutane sannan yayi printing da sauransu.
SATI NA BIYU (RANAR 8 ZUWA 14): Daga rana na 8 zuwa 14 wato kwanaki bakwai mutum ya koyi Control Flow wato irinsu If statement, da Kuma Loops irinsu For Loop, Do while da sauransu shima dai sau a goda misalai daban daban.
SATI NA UKU (RANAR 14 ZUWA 16): Daga ranar 14 zuwa 16 wato kwanaki 3 kenan sai mutum ya koyi Function da Kuma Modularization. Sai dai idan Language din irinsu Java ne ana kiran function da method, sai mutum ya koyi Method, yadda ake creating function da kuma ake kiransa wato Function Call. Sannan a goda misalai daban daban dan fahimtarsa da kyau
SATI NA UKU (RANAR 17 ZUWA 21): Daga ranar 17 zuwa 21 wato kwanaki biyar mutum ya koyi Data Structure irinsu Array shine babban al muhim aciki, amma ga yare irinsu Python da EasyBite akwai Dictionary da kuma Tuple. Duk da haka iya Array a ishi mutum a matsayinsa na Beginner, mutum ya dauki tsawon kwanaki biyar din dan fahimtarsa da kyau saboda nasan wuyarsa.
SATI NA HUDU (RANAR 22-30 KO 31): Daga nan mutum yafara yin kananun Projects, shi ne zai kai mutum ya zama Developer. Shi programming ba'a kwarewa akansa sai anayin project daban daban wato goda yin abubuwa. Misali lokacin da na koyi PHP abu na farko da nafara yi shine Social Network namar suna StuMeo. To haka yakamata mutum yayi, misali za'a iya yin wani abu kamar Calculator, ko Program na Gussing number, da Programming da zai zama yana da Login da Registration da kuma Profile da sauransu, sannu a hankali har za'akai ga chi.
Kaga amanta saboda saukake koyon Programming yasa na kirkiri EasyBite dan komai da komai bayanan EasyBite yana cikin wannan link din, sannan dadin dadawa EasyBite yafi duka yarukan da na irgo saukin fahimtar da mai koyon dan haka maza a garzaya
https://github.com/Dangujba/EasyBite
Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
04/04/2024.
Post a Comment