Milky Way Galaxy: nazari game da gungun Taurari dake sararin Samaniyar Subhana
Milky Way galaxy
Zamu iya fassara shi da 'Gungun taurari da ake kira, Milky Way'
Shekaru 100 da suka gabata, Milky Way Galaxy da ita kanta Kaunu(Universe) batu ne da masana suka yi ta tattaunawa akai wanda yaki ci yaki cinyewa. A 26 ga watan Afirilun 1920 masanin kaunu(Astronomer) mai suna Harlow Shapley bisa karancin sani irin nasa, yayi ikirarin cewa Milky Way Galaxy gaba dayanta shine Kaunu babu wani wuri kuma, wato duk Kaunu shine Milky Way Galaxy.
Cikin shekaru biyar, Masanin nan mai suna Edwin Hubble, ya gano wani gungun taurari(cluster) wanda suke da nisan da kowa a lokacin sai da ya yarda da shi cewa wadannan gungun taurarin da ya gano sun basu a cikin Galaxy kwata-kwata, wannan cluster din baya cikin Milky Way Galaxy, ashe wani gungun taurarin ne irin na Milky Way Galaxy wanda yake makotaka da Milky Way Galaxy, wanda aka laƙa masa suna da 'Andromeda Galaxy'. Bayan da Harlow Shapley ya ga binciken da Edwin Hubble ya yi, sai ya tabbatar da lallai wannan binciken ya rusa ikirarin sa na baya cewa; duka Kaunu shine iya cikin Milky Way Galaxy. Sai dai kuma ba duka ikirarin Harlow bane ya zama ba daidai ba, ikirarin sa na cewa Solar System yana da nisan gaske daga tsakiyar Milky Way Galaxy, an gano daga baya cewa gaskia ne wannan kam.
Menene Milky Way Galaxy
Milky Way Galaxy, gungun taurari ne da kuran burabutsai(dust) da sauran gases na sararin subuhana, Solar system din mu yana daya daga cikin wannan gungun taurarin, da dare idan sararin samaniya tayi tangarau zamu ga wani jerin gungun taurari mai duhu-duhu da kalan madara-madara(kaman yanda muke gani a cikin hoto na biyun nan) wannan dogon hadarin gungun taurarin da muke ganin nan daya ne daga cikin hannayen Milky Way Galaxy din mu da muke ciki.
Kalmar Milky Way Galaxy ta samo asalin ne daga addinin girka(greek) cewa wai Alliya Hera ce ta watsa ruwan nonon ta a sararin samaniya, bayan da mabiya addinin girkan suka ga wannan gungun taurarin mai duhu-duhu kalan madara-madara.
Daga kan doron kasa(Earth) muna ganin Milky Way Galaxy ne kaman wani band na taurari saboda muna kallon sa ne daga cikin Milky Way Galaxy din, yasa ba zamu iya ganin hakikanin siffar sa mai kama da farantin disk ba.
A shekarar 1610 Galileo Galilie yayi amfani da tabaran hangen nesan sa(telescope 🔭) wurin iya rarraba wannan band din gungun taurarin, wanda a gani na zahiri ba tare da amfani da telescope ba ba zamu iya rarrabe wadannan taurarin ba.
Milky Way Galaxy, yana da siffar(shape) farantin disk, da hannaye guda hudu da suka faro daga tsakiyar sa, wanda ake kiran siffar su da 'spiral shape' Milky Way Galaxy yana da kaurin kiman nisan 100 light-years(light years shine nisan tafiyan haske cikin sararin subuha na tsawon shekara guda, wato kwatankwacin nisan kilomita tiriliyan 9.46) 100 light years yana da nisan kilomita tiriliyan 946 kenan, sannan Milky Way Galaxy yana da fadin 150,000 light years, wato nisan kilomita tiriliyan 9.46 sau 150,000 shine daidai da 1,419,000,000,000,000(Quadrillion ɗaya da trillion ɗari huɗu da shatara) tirkashi!
Milky Way yana da yawan taurarin da ya kai sama da biliyan 100 zuwa 400, kusan ko wani tauraro yana da kwatankwacin duniyar planet guda daya, kar a manta Rana(wanda) muke ganin sa yana cikin taurarin da suke daya daga cikin hannayen Milky Way Galaxy wanda ake kira da 'Orion Spur'(Rana da muke ganin sa shima tauraro ne, haka sauran taurari suke, kawai banbancin su shine girma da sauran chemicals din da suka kumsa, sauran taurarin da muke kallon su kaman kananu ne, suna da girman jiki matuka sosai, da yawan su girman su yafi girman Ranan mu sau biliyoyi, dalilin da yasa muke ganin su kanana, shine saboda sunyi nisa ne sosai da mu, tauraro mafi kusa da mu shi ake kira da, Alpha Centuari yana da nisan 4 light years. Rana da muke ganin sa yana da fadin nisan kilomita miliyan 1.4, zamu iya jera duniyar mu da muke kai(Earth) guda 109 daga bangare daya zuwa dayan bangaren a fuskan Ranan, daya daga cikin taurarin da suka fi Ranan mu girma akwai Pistol Star wanda yake da nauyi sama da nauyin Ranan mu sau 100, hasken sa kuma ya fi hasken Ranan mu sau miliyan 10, tauraro mai suna UY Scuti radius(faɗinsa daga tsakiyar sa) yafi na rana sau dubu 1,700). Milky Way yana da hannaye guda hudu kamar haka;
Hannu mai suna Scutum-Centaurus
Hannu mai suna Norma
Hannu mai suna Sagittarius
Hannu mai suna Perseus
Sai kuma Hannun Orion spur ta inda solar system din mu yake kenan, yana nan ta wuraren hannun perseus, bayan hannun Perseus kuma akwai wani hannu da ake kira Outer Arm.
Nisa tsakanin Duniyar mu ta Solar System da tsakiyar Milky Way Galaxy tana da kusan nisan 25,000 light-years kwatankwacin kilomita 2,365,000,000,000,000, Milky Way Galaxy ya wanzu ko ya samu ne shekaru biliyan 13 da suka gabata, bayan kusan shekaru biliyan ɗaya da aukuwar Big Bang(samuwar Kaunu). Galaxies sun kumshi gungun taurari, da burabutsai(dust) da dark matter wanda karfin force na Gravity ya tara su wuri guda, masana Astronomy har yanzu basu da tabbacin yaya Galaxy ya faro, sai dai kuma bayani mafi saukin fahimta ya nuna cewa, Gravity ne ya rika janyo burabutsai da gases wuri guda har aka samu taurari(kamar yanda muka yi bayanin yanda aka samu tauraron mu(Rana) da sauran duniyoyin Planets) haka shima Galaxies Gravity ne ya harhaɗe wadannan burabutsai da gases ya yi ta juya su cikin tsananin juyi har suka zama wutan mai kamar dunkulen kwallo da yanzu muke ganin su a matsayin taurari, ya rika har-haɗe su wuri guda da muke ganin su a matsayin Galaxies, constellations, Solar Systems da sauran gungun abubuwa irin su Nebula da sauran su, a takaice dai kusan duka kaunun force na Gravity ne ya rike shi.
Milky Way Galaxy, mai shekaru biliyan 13 yana daya daga cikin galaxies 50 da suke wani gungun galazzozi da ake kira 'Superclusters'. Triangulum Galaxy da Andromeda Galaxy ne suke da girma kwatankwacin girman Milky Way Galaxy, sauran Galaxies din kananan Galaxies ne, a tsakiyan Milky Way Galaxy din mu akwai wani babban Black Hole da ake kiran sa da 'Sagitarrius A*' yana da nauyin rana sau miliyan 4, duka taurarin cikin Milky Way Galaxy (har da ranan mu) suna yi wa wannan Black Hole din ɗawafi sau daya cikin shekaru kusan miliyan 220 zuwa miliyan 360 cikin saurin kilomita 555.2 a ko wani dakika(second)
Zamu da kata anan, in an ji daɗin karatu a taya mu sharing domin wannan shafi ya samu karɓuwa. Mun Gode!
Post a Comment