Clifford Oche Agbo Ella, wanda aka fi sani da Miss Sahhara shi ne Namiji na farko da ya canja jinsi ya koma mace a tarihi
Miss Sahhara (wanda aka yi masa lakabi da Miss saHHara ) mawaƙiyar Najeriya ce da Biritaniya, kuma sarauniyar kyakkyawa kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam.
Tare da halartarta gasar Miss International Queen a shekarar 2011, gasar da aka shirya don mazan da suka canja halitta, Miss Sahhara ya zama mace ta farko daga Najeriya da ta fito a cikin labaran duniya. Daga baya ta kafa wata ƙungiyar wayar da kan jama'a ta duniya da ake kira TransValid.
A cikin 2014, ta zama mace baƙar fata ta farko da ta yi nasara a gasar kyau ta duniya lokacin da ta sami kambin Super Sireyna Worldwide 2014 a kasar Philippines.
Post a Comment