. Haka wata baiwar Allah tace min ita fa sai taga kamar ana bibiyar wayarta kuma cikin ikon Allah da na karɓi wayar na duba sai naga tabbas an saka mata Application ɗin da ake bibiyar wayar nata kuma bayan ansaka Application ɗin sai aka ɓoyeta ta yadda bazaka taɓa gane ansaka wani abu ba.
Sai na cire mata, kuma nashiga setting na duba naga ana Forwarding duk wayar da takeyi zuwa wata number, itama na cire mata.
Domin kare kai daga faɗawa irin wannan ko kuma idan kaima kana tunanin ana bibiyarka abinda zakayi shine kaje cikin wayarka kashiga Setting, bayan kashiga zai buɗe maka zakaga wurin da aka rubuta "Security" sai kashiga yana buɗewa sai ka danna wurin da aka rubuta "Device Admin App" anan ne zaka tsaya ka lura sosai duk wata Application da take aiki akan wayarka zakaganta a wurin anyi Activating nata, idan kaga Application ɗin da bakasan da ita ba kuma anyi Activating ɗinta sai kawai kayi Deactivating ɗinta a wurin, insha Allah shikenan, idan ma wayarka ake bibiya shima sai kashiga wurin "Call Forwading" a cen wurin "Call Setting" duk number da aka saka take bibiyar wayar naka zakaganta a wurin sai kawai ka cireta.
Ina fatan wannan zai taimaka?
🙏
@Salisu Aburrazak sahel
Post a Comment