Asali da tarihin samuwar Kalmar Yahoo ko Yahoo boy/boys
Kalmar "Yahoo-Yahoo" kalma ce da akeyi ma Cyber Criminals ko Froudsters a Africa laƙabi da ita, amma kana fita Africa kaje wata ƙasar kace masu ai wane ɗan Yahoo ne, zasu tambayeka menene kuma Yahoo..😀
A africa ɗin ma ba kalmar Yahoo Boys kaɗai bace ake amfani da ita wurin kiran Cyber Criminals ba ana amfani da Gee Boys, Yahoo Boys, da Sakawa Boys, kuma tabbas Nigeria itace ta ɗaya a Scamming ko Cyber Crime a Africa kuma itace ta ukku a duniya wurin aikata laifukan Internet da akeyi (Cyber Crime).
Sannan itama kalmar 419 a Nigeria aka samar da ita ana nufin masu dabaru domin ƙwashe ma mutane dukiya a Internet irin masu amfani da dabarar yaudara da akafi sani da Social Engineering da kuma ta hanyar Phishing, duk waɗannan mutanen a Africa ana kiransu da yan 419, amma asalin kalmar 419 daga cikin kundin hukunta laifukan Internet aka samota wato Nigerian Criminal Code Act; akwai Section 419 anan ne dokar ta samo asali sai aka dinga amfani da Lambobin ga masu aikata laifin.
Bari dai mu koma baya muyi bayani akan dalilin yin Posting din, Asalin kalmar 'Yahoo' mail ne dake bada damar aika saƙo zuwa ga wanda kakeson tura ma saƙon kamar dai yadda gmail yake, tun january 1994 aka samar da wannan mail na yahoo wajajen shekara 30 kenan yanzu, sunada Headquarter nasu a California, United State da sauransu, kuma sannan ana amfani da "Yahoo Mail" a duniya bakiɗaya (Worldwide), kamfanoni guda biyu ne suka haɗu suka samar da wannan Fasaha ta "Yahoo Mail" da kamfanin Apollo Global Management wanda sune sukeda 90% na kaso a kamfanin sai kuma kamfanin Verizon Communications sunada 10% ɗin, Jerry Yang da David Filo suka ƙirƙiri wannan fasahar ta "Yahoo Mail" a ƙarƙashin Fasahar Yahoo Mail sunada ma'aikata mutum 8,600, idan kanason buɗe Yahoo Mail kamar yadda ka buɗe Gmail naka domin duk aikinsu ɗaya ne, to zaka shiga Yahoo.com sai ka cike Form ka buɗe Account dasu.
A ƙarƙashin wannan fasahar ta "Yahoo" akwai "Yahoo News", "My Yahoo", "Yahoo Mail", "Yahoo Finance", da "Yahoo Sports".
Dan haka a matsayinka na wayayye a cikin ilimin fasaha bakinka ya saba da kiran waɗannan mutane da Cyber Criminals, Fraudster ko Scammers, kar naji kace Yahoo Boys Idan ba haka ba na buge bakin..😀😁
© Salisu Abdurrazak Saheel
إرسال تعليق