Alaka Tsakanin Tahajjud, da Tafsiri a Ramadhan, da Musabaqan Alkur'ani bidi'o'i ne kamar Maulidi.
Wasu suna nuna cewa; Tahajjud, da Tafsiri a Ramadhan, da Musabaqan Alkur'ani bidi'o'i ne kamar Maulidi.
To miye alaka tsakanin wadannan, da har hukuncinsu zai zama daya?
Ita Musabaqa ba ibada ba ce, don haka ba za a ce mata bidi'a ko Sunna ba, saboda a babin halal da haram take. Amma ita halal ce ja'iza, saboda tana da asali a Shari'a.
Amma shi kuma Tahajjud da Tafsiri duka biyu ibada ne, kuma kowanne daga cikinsu yana da asali a Sunna.
Shi Tahajjud asalinsa daga Annabi (saw) ne, kamar yadda ya zo a Hadisan A'isha (ra), Abu Zarr (ra) da wasunsu. Haka kuma Sahabbai sun yi.
Shi kuma Tafsiri Annabi (saw) yana Darasin Alkur'ani tare da Mala'ika Jibril (as) a kowane dare na watan Ramadhan. Kuma ya tabbata a Hadisi; Sunna ne mutane su taru a Masallaci suna karanta Alkur'ani, suna darasinsa. Don haka Tahajjud da Tafsiri suna da asali a Sunna, ba za a kira su da bidi'a ba.
Amma shi kuma Maulidi fa?
Shi ma ibada ne, amma sai dai ba shi da asali a Sunna, don haka ya zama bidi'a.
Sau da yawa mutane sukan yi kuskure wajen fahimtar hakikanin bidi'a. Ita bidi'a ita ce ibadar da ba ta da asali (dalilin shar'anci) a Addini.
Saboda haka, Tahajjud da Tafsiri ba bidi'a ba ne, bidi'a bisa ma'ana ta Shari'a, amma shi kuma Maulidi bidi'a ne, bata ne, saboda ba shi da asali a Sunna da Shari'a.
إرسال تعليق